NLC Ta Musanta Janyewa Daga Zanga-zangar Tsadar Rayuwa Da Ake Shirin Yi
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC ta musanta ikirarin cewa ta janye daga zanga-zangar kasa da ake shirin gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta inda ta bayyana rahotanni a matsayin “karya.”
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumuntanta na X, NLC ta fayyace cewa ba za ta iya janyewa daga zanga-zangar da ba ta shirya ba
“Masu shirya zanga-zangar ta kasa ce kawai za su iya yanke shawarar janyewa ko ci gaba da zanga-zangar,” in ji NLC.
Sanarwar ta bayyana cewa “Kungiyar Kwadago ta Najeriya tana da hanyoyi musamman hanyoyin yanke hukunci kan jagoranci wanda ayyukanta na masana’antu kamar zanga-zangar ke bi kafin a gudanar da irin wadannan ayyukan,”
NLC ta kuma nuna goyon bayanta ga zanga-zangar da ake shirin gudanarwa, tare da amincewa da mawuyacin halin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta saboda manufofin gwamnati.
“Kasancewar NLC da cewa ba ita ta shirya zanga-zangar ba, hakan ba ya nufin kungiyar ta manta da halin ƙuncin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki sakamakon munanan manufofin tattalin arziki na gwamnati,” in ji kungiyar ta NLC.
NLC ta buƙaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tattaunawa da jagororin zanga-zangar domin biyan bukatunsu inda ta ba da shawarar a guji amfani da ƙarfi wajen mayar da martani ga rashin jin dadin jama’a.