Labaran Duniya

Sakataren gwamnatin tarayya da ministocin Tinubu na taron gaggawa kan zanga-zangar da aka shirya yi a faɗin Najeriya 

Sakataren Gwamnatin Tarayya SGF George Akume a halin yanzu yana ganawa da Ministoci a kan zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki da ƴan Najeriya suka shirya yi a faɗin ƙasar.

Taron wanda ke gudana a bayan fage ya samu halartar Ministoci da dama daga cikin Ministocin Shugaba Bola Tinubu.

Wasu daga cikin Ministocin da suka halarta sun haɗa da Nyesom Wike Ministan Abuja, da Yusuf Tuggar Ministan Ma’aikatar Harkokin Waje, da Zephaniah Jisalo Ministan Ayyuka na Musamman, da Tahir Mamman Ministan Ilimi, da kuma Abubakar Bagudu Ministan Kasafin kuɗi da tsare-tsare.

Sauran sun haɗa da Wale Edun Ministan Kuɗi, da Mohammed Idris Ministan yaɗa labarai, da Bello Matawalle Ministan Tsaro, da David Umahi Ministan ayyuka, da mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Nuhu Ribadu da sauransu.

Idan ba a manta ba a ranar Talata ne Shugaban ƙasar ya roki ƴan Najeriya da su yi watsi da zanga-zangar nuna adawa da salon Gwamnatinsa da za a fara ranar 1 ga watan Agusta.

Zanga-zangar adawa da tabarbarewar tattalin arziki da aka shirya ta dauki hankula sosai a shafukan sada zumunta inda ake shirin gudanar da ita a faɗin Jihohin Najeriya 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button