Labaran Duniya

Dan Majalisar Tarayya A Jihar Zamfara Ya Ziyarci Yankunan Shi Na Karamar Hukumar Bungudu Da Maru

A Ranar Jumu’ah din data gabata ne Bayan shafe makonni uku na wasu muhimman ayyuka masu tasiri a wajen kasar nan da kuma a nan Najeriya, Dan Majalisar tarayya Abdulmalik Zubairu Bungudu ya samu damar ziyartar mazabar Yankunan Shi Na Bungudu da Maru.

A yayin ziyarar, na kai ziyarar jaje ga wasu al’ummomi da sukayi fama da Matsalar ‘yan fashi da makami. Wadannan al’ummomi sun hada da; Garin Ka’ida dake unguwar Bela/Rawayya inda aka kashe mutane 4, aka Kuma yii garkuwa da Akalla mutun 43 tare da jikkata wasu.

“Hakazalika mun ziyarci garin Danguro da ke yankin Nahuche a ƙarkashin Karamar Hukumar mulki ta Bungudu inda akai-akai hare-haren ‘yan fashi da makami har ya tilasta musu barin gidajensu”.

Hakika ziyarar ta bayyana mana hakikanin halin da mutanen mu suke ciki. 

Insha Allahu za mu ci gaba da lalubo hanyoyin da za mu iya rage radadin da talakawa da mazauna karkara ke ciki, Inji Shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button