Peter Obi Yace Ya Na Goyon Bayan Masu Shirin Fita Zanga-zanga
Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi ya ce yana goyon bayan masu shirin fita zanga-zanga ranar 1 ga watan Agusta don adawa da tsadar rayuwa.
Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra, ya ce kundin tsarin mulki ya bai wa ƴan ƙasa damar yin zanga-zanga.
Sai dai, ya yi gargaɗi kan tayar da hankali, inda ya ce ya kamata a yi zanga-zanga yadda doka ta tanada.
Ya ce yunwa da rashin madogara na cikin abubuwan da suka sa matasa ke shirin fita zanga-zanga, inda ya yi kira ga hukumomin Najeriya da su fito domin tattaunawa da matasan da kuma jin kukansu.
“Abubuwa sun yi matukar wahala a ƙasar nan. Ya kamata mu saurari korafe-korafen ƴan Najeriya,” in ji Obi.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su bai wa masu zanga-zangar kariya, sannan kada su wuce gona da iri.