Gwamnatin Tarayya Zata Fara Sayarwa Matatar Dangote Danyen Mai A Farashin Naira
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta fara sayarwa matatar Dangote ɗanyen mai a Naira, a wani yunkuri na tabbatar da daidaiton farashin man fetur da kuma farashin Dala da ta Naira.
Ta sanar da haka ne a yau Litinin bayan taron majalisar zartaswa ta tarayya da aka gudanar.
Matatar Dangote dai na buƙatar jiragen ruwa 15 na danyen mai a kan farashin dala biliyan 13.5 duk shekara.
Amma kamfanin mai na NNPC na samar da huɗu a yanzu.
Sai dai majalisar ta amince da cewa a sayar da mai ganga 450,000 da za a yi amfani da shi a cikin ƙasar a Naira ga matatun Najeriya, ta hanyar fara wa da matatar Dangote.
Bankin Afrexim da sauran bankuna a Najeriya za su jagoranci kasuwancin tsakanin Dangote da NNPC.
Ana ganin hakan zai taimaka ainun wajen rage wa ƙasar biliyoyin dala da take kashewa wajen shigo da tataccen mai.