Majalisar Wakikan Najeriya Zata Katse Hutunta Don Tattauna Muhimman Al’amuran ƙasa
Majalisar wakilan Najeriya za ta katse hutunta na shekara domin yin wani zama a ranar Laraba da nufin tattauna muhimman batutuwan da suka buƙaci majalisar ta yi magana a kan su.
Bayanin hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa daga magatakarda na majalisar Yahaya Danzaria.
Taron zai ƙunshi tattaunawa da matasa ƴan Najeriya a wani taro da kakakin majalisar Tajuddeen Abbas zai karɓi baƙunci.
Taron zai haɗa da shugabannin matasa da ɗalibai daga manyan makarantu da ƙwararru matasa da kuma wakilai daga ƙungiyoyin matasa da ƙungiyoyin farar hula.
An tsara taron domin bai wa matasa ƴan Najeriya damar bayyana damuwarsu su kuma bayyana ra’ayoyinsu sannan su tattauna da jagororin majalisa kan matsalolin da suka shafi rayuwarsu da kuma gobensu.
Majalisar wakilan ta soma hutu ne ranar Talatar da ta gabata inda ta shirya dawowa ranar 17 ga watan Satumba.
Shi ma shugaban majalisar dattijai, Sanata Godswill kpabio ya kira taron gaggawa don tattauna al’amuran ƙasar, kamar yadda sanarwa daga magatakardan majalisar, Chinedu Akubueze ta bayyana.
Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani ba game da abin da taron zai mayar da hankali a kai.
Za a yi taron ranar Laraba, 31 ga watan Yuli, kwana ɗaya kafin gagarumar zanga-zangar da aka shirya yi a faɗin Najeriya.