Labaran Duniya

Ministan Ilimi A Najeriya Ya Shawarci Daliban Jami’o’in Kasar Da Su Tsame Kansu Daga Zanga-zanga

Ministan ilimin Najeriya, ferfasa Tahir Mamman ya shawarci dukkan ɗaliban jami’o’i su kasance cikin jami’arsu a lokacin zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar.

Ministan ya bayar da shawarar ne cikin wata sanarwa da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa ta fitar a yau Litinin da ke ɗauke da sa hannun muƙaddashin babban sakataren hukumar.

Ministan ya ce ya bayar da shawarar ne saboda baya son ɗaliban su saka rayuwarsu cikin haɗari.

“Gwamnatin Najeriya na sane da ƴancin ƴan ƙasa kan gudanar da zanga-zanga ta lumana amma ta fi damuwa da tsaro da kuma kwanciyar hankalin ma’aikata da na ɗalibai da jami’o’i idan ana zanga-zanga” in ji sanarwar.

“Saboda haka ne ministan ilimi ya umarci shugabannin jami’o’i da su tabbatar da tsaro da kuma tsaron al’ummar jami’a ballantana na ɗalibai da na ma’aikata.”

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da tsananin yunwa a faɗin ƙasar daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button