Shugaba Tinubu Masoyin Arewa Ne, Goyon Bayan Mu Yake Buƙata Don Ciyar Da Yankin A Gaba Ba Zanga-zanga Ba
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bukaci ‘yan Najeriya da su marawa manufofi da shirye-shiryen Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya, yana mai jaddada cewa Shugaban ƙasar yana da kyawawan manufofi ga Najeriya.
Sanata Kashim Shettima ya kuma yi nuni da cewa sabanin rade-radin da ake yi cewa, Shugaba Tinubu baya ƙaunar yankin Arewa ko kuma baya son musulumi, yana mai cewa shugaban ƙasar cikakken mai kishin Arewa ne kuma baya nuna ƙiyayya ko wariya ga kowa bugu da ƙari idan aka yi duba da nade-naden ‘yan Arewa a manyan mukamai da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da yayi hakan ya cire duk wani zargi,
Mataimakin Shugaban ƙasar ya kuma ja kunnen masu niyyar fita zanga-zanga, yana mai bayyana cewa duk da dai cewa yancin kowa ne to amma illar da take iya haifarwa abar fargaba ne musamman idan aka yi dubi da yadda wasu gurɓatattu ke amfani da zanga-zangar wajen cimma wasu munanan manufofinsu. A maimakon haka, ya karfafa matasa da su bi hanyar tattaunawa da kuma goyon bayan shirye-shiryen gwamnatin da nufin kawo sauyi ga rayuwar ‘yan Arewa da Najeriya baki daya.
Haka zalika ya bayyana wasu shirye-shirye da suka hada da tsarin sake tsugunar da mutanen da rikici ya rutsa da su da kuma ma’aikatar kula da kiwo, a matsayin misalan irin sadaukarwar da shugaba Tinubu ya yi wa Arewa.
Shettima ya kuma yi kira ga masu yada labarai musamman na yankin Arewa da su hada kai da Gwamnati wajen wayar da kan al’umma da sanar da su kyawawan manufofin Gwamnatin don bunkasawa da ciyar da yankin gaba, yana mai jaddada cewa “wannan ba lokacin zanga-zanga bane, lokaci ne na mu haɗa kai mu goyi bayan ci gaban yankin mu”