Labaran Duniya

Ƙasar Rasha ta nesanta kanta daga duk wasu masu ɗaga tutocin ƙasarta a zanga-zangar da ake yi a Nijeriya.

Tun bayan fara zanga-zangar ranar 1 ga watan Agustan nan ne aka dinga ganin gungun mutane a jihohi da dama a fadin ƙasar suna ɗaga tutar ƙasar Rasha a yayin tattakin.

Masu sharhi kan harkokin yau da kullum sun yi ta jan hankalin ‘yan Nijeriya a kafafen watsa labarai da shafukan sada zumunta cewa hakan illa ne ga dimokradiyyar ƙasa mai cikakken ‘yanci irin Nijeriya wadda take ƙarƙashin mulkin siyasa.

A sanarwar da ya fitar a yau Litinin, Ofishin Jakadancin Rasha da ke Nijeriya ya ce “mun lura da rahotannin da kafafen watsa labaran Nijeriya ke fitarwa da kuma yaɗuwar wasu hotuna da bidiyoyi a intanet da ke nuna masu zanga-zanga a arewacin ƙsar suna ɗaga tutocin Rasha suna kiran sunan Shugaba Vladimir Putin.

“Gwamnatin Tarayyar Rasha da kuma wasu jami’an Rasha ba su da hannu a cikin waɗannan ayyukan ta kowace hanya. Kamar kullum, muna jaddada cewa Rasha ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ƙasashen waje ciki har da Nijeriya,” in ji sanarwar.

Rasha ta ƙara da cewa “wannan aniyar ta masu zanga-zangar ta ɗaga tutocin Rasha zaɓi ne na ɗaiɗaikun mutane, kuma ba sa nuna wani matsayi ko manufofin gwamnatin Rasha kan batun.

“Muna mutunta dimokuradiyyar Nijeriya kuma mun yi imanin cewa zanga-zangar lumana bisa ga dokar Nijeriya alama ce ta dimokradiyya. Duk da haka, idan waɗannan abubuwan sun haifar da duk wani rikici ko tashin hankali za mu yi Allah wadai da su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button