Shugaba Tinubu Ya Nada Shuwagabannin Ma’aikatar Jinkai Da Kyautata Rayuwar Al’uma Ta Ƙasa
A ƙoƙarinsa na ganin shirin tallafawa al’umma ya gudana yadda ya kamata, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugabannin ma’aikatar jinƙai, agaji da kyautata rayuwar al’umma ta ƙasa. “Federal Ministry of Humanitarian Affairs, Disaster Management and Social Development”.
Mutanen da shugaba Tinubu ya naɗa sun haɗa da:
1. Dakta Badamasi Lawal, a matsayin shugaban shirin samarwa al’umma jari “National Social Investment Programme Agency (NSIPA)”. Dakta Lawal yana da digirin digirgir a fannin ilimi, kuma tsohon kwamishinan ilimi ne a Jihar Katsina.
2. Funmilola Olotu, a matsayin shugabar shirin kula da al’umma. Tana da digirin digirgir a fannin kasuwanci, sannan kuma, babbar mataimakiya ce ta musamman ga gwamnan Jihar Legas.
Sauran sun haɗa da:
3. Aishat Alubankuɗi, mai kula da shirin tallafawa masu buƙata ta musamman.
4. Princess Aderemi Adebowale, mai kula da shirin ciyar da ɗalibai.
5. Malam Abdullahi Alhassan Imam, mai kula da shirin ba da tallafin rage raɗaɗi.
6. Misata Ayuba Gufwan, babban sakatare na ma’aikatar kula da sha’anin masu buƙata ta musamman.
7. Lami Binta Adamu Bello, daraktar hukumar yaƙi da safarar ɗan’adam.
Shugaba Tinubu ya buƙaci su gudanar da ayyukansu cikin nagarta da ƙwarewa su tabbatar ƴan Najeriya musamman masu ƙaramin ƙarfi sun amfana.