Akalla Kimanin Matasa Milyan 1.4 Ne Za Su Sami Aikin Yi A Shirin Gwamnati Na Farfado Da Masana’antar Auduga
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani gagarumin shiri na farfado da masana’antar auduga a Najeriya, da nufin samar da ayyukan yi sama da miliyan 1.4 a duk shekara a fannin.
A cewar wata sanarwa da ta fito daga ofishin mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima, shirin na hadin gwiwa ne tsakanin gwamnati da kwamitin ba da shawara kan auduga (ICAC).
Da yake jawabi a wajen wani taro da jami’an ICAC, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya jaddada bukatar ganin masu ruwa da tsaki sun hada kai don bunkasa darajar auduga a fannonin da suka hada da noma, saka, ciyawa, da murza auduga.
Matakin wani bangare ne na yunkurin gwamnati na samar da masana’antu, da nufin samar da damammakin aiki a fannin sana’ar auduga.
Gwamnonin jihohin Legas da Imo da suka halarci taron, sun nuna goyon bayansu ga shirin tare da yin alkawarin hada kai da masu ruwa da tsaki domin bunkasa fannin.
ICAC ta yi alƙawarin bayar da shawarwari na ƙwararru da goyan baya don haɓaka yawan aiki da dawo da kimar masana’antun audiga da sauƙaƙe saka hannun jari a fannin
Ana sa ran farfado da masana’antar auduga zai yi tasiri sosai ga tattalin arzikin Najeriya da samar da ayyukan yi da ma kawo sauyin tattalin arziki.