Labaran Duniya

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Yace Wasu Yan Siyasa Ne Suka Agazawa Masu Zanga-zanga Don Kawo Fitina

A cikin makon da ya gabatan ne mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya zargi wasu ‘yan siyasar ƙasar da taimaka wa masu zanga-zanga domin haddasa ruɗani a ƙasar.

Shettima ya fadi hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa a ranar Alhamis, yayin da wasu ‘yan ƙasar suka shirya zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a ƙasar.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce shugaban ƙasar na fifita arewa idan aka yi la’akari da sabuwar hukumar kula da dabbobi da shugaban ƙasar ya samar saboda ƴan arewa su amfana ne, da kuam wasu muhimman muƙaman ministoci da ya bai wa ‘yan yankin.

”’Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na sane da halin da al’umma ke ciki, kuma yana tausaya masu, Insha Allah gwamnati na kawo tsare-tsaren ganin cewa al’ummarmu an ɗauki matakin ƙarfafasu,” kamar yadda Shettiman ya bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button