A kalla Yan Bindiga Talatin Ne Suka Mutu A Yayin Wani Rikici Da Ya Barke A Tsakanin Su Wurin Raba Dabbobi Da Suka Sato
Wani kazamin rikici da ya barke a tsakanin yan bindiga a Jihar Zamfara ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 30 daga cikin su, wasu kuma suka samu munanan raunuka.
Lamarin ya faru ne a kauyen Kawaye dake Karamar hukumar mulkin Anka a Jihar ta Zamfara kamar yadda wani mazaunin wurin da ya nemi a sakaya sunan shi ya ce, fadan ya tashi ne a lokacin da yan bindigar ke rabon shanun da suka sato.
“Barayi ne sun koro shanu daga Arewa, to, wurin rabon shanun sai aka baiwa wasu yan kadan wasu aka basu masu yawa, shine sai fada ya barke a tsakanin su, suka dinga musayar wuta, an kashe barawo zai kai talatin (30), yanzu haka akwai wasu da zasu kai ashirin suna jinya,” in ji shi
Har ila yau ya ce an yi fadan ne a Dajin Kawaye, tsakanin yaran wasu manyan yan bindigar wato yaran Kachalla Halilu da yaran Bello Kaura, ya ce sun ji lokacin da ake musayar wutar kuma sun gano adadin wadanda aka kashen ne ta hanyar labarin da yaran yan bindigar ke yi har ya iso a kunnuwan su.
Shi ma wani mazaunin wani kauyen da ke makwaftaka da wajen da lamarin ya faru, ya ce rikicin har ya shafi wasu masu wankin zinari a dajin wadanda har sashen yan bindigar dake yakar junan su ya riske su.
“Sun sato shanu da rakumma sun fi 1000 daga yankin Sakkwato, wurin rabon su ne suka samu rashin fahimtar juna har fada ya faru a tsakanin su, kuma sun yi barna sosai don sun harbi mutane da dama, don ina ganin yanzu akwai kusan mutun 17 kwance a asibitin Nasarawa,” a cewar wani mazaunin yankin.
To Sai dai duk kokarin da wakilin Sashen Hausa na muryar Amurka ya yi don jin ta bakin rundunar yan sanda dake jihar abun ya ci tura, domin duka kiraye kirayen waya da gajerun sakonni da ya aikawa kwamishin yan sandan jihar CP Shehu Muhammad Dalijan bai samu amsar sakonnin ba.
Amma wani dan jarida mai zaman kan shi kuma mai bincike akan ayukkan yan bindiga a jihar Zamfara Mannir Sani Fura Girke, ya ce rikicin ya samo asali ne a tsakanin barayin daji, wato yaran Kachalla Halilu da yaran Bello Kaura wanda shine babban yaron gawurtaccen barawon dajin nan da Sojoji suka kashe a watannin baya wato Alhaji Sha-Dari.
“Bayan sun je sun sato dabbobi a karamar hukumar Mulkin Gummi a Jihar Zamfara da kananan hukumomin Tureta da Shadari a Jihar Sokoto, to sun zo kusa da Kauyen Kawaye domin su raba Dabbobin da suka sato, yadda akayi rabon ne bai ma wasu dadi ba,Sai rikici ya tashi.” In ji Mannir Sani Fura-Girke.
Mannir ya ce binciken da ya yi ya gano cewar a sakamakon harbe harben da suka yi a tsakanin su, an kashe barawo kusan ashirin a kowane bangaren kuma an raunata kusan guda talatin (30).
Wannan harbe harben da suke yi na mai kan uwa da wabi, shine ya shafi wasu masu wankin zinari, har Allah ya yiwa wasu daga cikin su rasuwa, in ji shi.
Ya zuwa yanzu dai wasu bayanai na nuna cewar, ana cigaba da samun karuwar barkewar rikici a tsakanin yan bindigar a Jihar Zamfara, yayin da kuma suke cigaba da zafafa hare hare a kan al’ummar jihar ko dai don yin kisa ko satar dabbobi ko kuma yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.