Labaran Duniya

FCCPC A Nijeriya Zata Fara Zama Da ‘Yan Kasuwa Domin Nazarin Farashi

Hukumar Kula da Hakkin Masu Saye da Amfani da Kayayyaki a Nijeriya FCCPC ta ce za ta fara wani zama da shugabannin ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a samar da sayar da kayayyaki a faɗin ƙasar, a wani ɓangare na wani shirin bincikar yadda ake tsauwala farashin kayayyaki ba tare da bin ƙa’ida ba.

A sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, FCCPC ta ce duk da cewa an san farashin canjin kuɗaɗen waje ya yi tasiri ga darajar Naira, amma ta lura da yadda ake tsauwala da yin ƙumbiya-ƙumbiya a farashin kayayyakin da ake shigar da su ƙasar da ma wadanda ake yi a cikin gida, fiye da ƙima.

“Wannan rashin adalcin ya zama ruwan dare a sha’anin kasuwanci a ƙasar, inda wasu ƙungiyoyin ‘yan kasuwa ke ƙayyade farashi mai yawa don tatsar masu saye,” in ji sanarwar.

Hukumar FCCPC ta ce ta yi amanna yin aiki tare da shugabannin ‘yan kasuwa zai sa a samu fahimtar juna kan samar da farashi mai ma’ana na kayayyaki tare da daƙile cin ƙazamar riba da ake yi a kan masu sayayya a lokacin da ake fuskantar kalubalen tattalin arziki.

FCCPC ta ce za ta ci gaba da ɗabbaka irin wannan hulɗar da shugabannin ‘yan kasuwa don haɓaka ingantacciyar al’adar cinikayya ba tare da sanya masu sayen kaya a cikin tasku ba.

“Tuni dai Hukumar ta umurci masu gudanar da manyan kantuna da su fayyace farashin kayayyakinsu da suke kan kantocin shagunansu don masu saye su dinga gani ɓaro-ɓaro domin kauce wa ƙumbiya-ƙumbiya da kuma kauce wa yi wasu masu sayayya ba-zata ta hanyar hana su ganin kudin kaya har sai sun kammala ciniki sannan su gani a rasiti.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button