Labaran DuniyaUncategorized

An Hannunta Kyautar Transifoma Ga Al’umar Garin Mayanci Domin Inganta Hasken Wutar Lantarki A Garin

DAGA SHAMSU BELLO BUNGUDU

Ayau Alhamin ne 15 ga watan Agusta na Shekarar 2024 wani Kwamiti ƙarkashin jagorancin Tsohon Shugaban Jam’iyar APC na Karamar Hukumar mulki ta Bungudu Alhaji Bashar Bello Auki suka Hannunta Kyautar Transifoma Ga Al’umar Garin Mayanci wadda Dakta Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu yasiyawa Al’umar garin.

Wannan Kyautar tabiyo Bayan korafin da Al’umar garin na Mayanci sukayiwa Dan Majalisar dake wakiltar Kananan Hukumomin Bungudu da Maru a majalisar tarayya ta Najeriya Dakta Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu.

Kwamitin yace sun Hannunta trasifomar sabuwa Mai Lamba 330 KVA ga al’umar na gundumar Mayanci dake ƙarkashin Karamar Hukumar mulki ta Maru.

Al’umar yankin garin Mayanci sunyi godiya sosai ga wannan Kwamiti dakuma Basu Sakon isar da muhimmiyar godiyar su ga Dakta Abdulmalik Zubairu Bungudu akan wannan Abun Alkhaeri dayayi masu.

Kananan Hukumomin Bungudu da Maru dai na Daya daga cikin yankin dake alfahari da wakilin nasu a majalisar wakilai ta kasa, inda suke ta Addu’o’in Sanya Albarka ga Dan majalisar da Kuma yimasa fatan Alkhaeri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button