Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed Yace Idan Jonathan Zai Dawo Takarar Kujerwr Shugaban Kasa 2027 To Zai Janye Masa
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ce yana tunanin tsayawa takarar shugaban kasa amma zai yi watsi da burinsa idan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yanke shawarar tsayawa takara.
Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan wata kungiya mai zaman kanta NGO, ta bukaci ya yi tunanin tsayawa takarar shugaban kasa.
A cewar gwamnan, Jonathan yana da gogewa kuma zai yi aiki mai kyau idan ya samu ikon tafiyar da kasar.
“Game da kiran da kuka yi na in gabatar da kaina, har yanzu ina tunanin damata a matsayina na jagoran ‘yan adawa.
“Na san akwai shugabanni nagari a cikin PDP, musamman maigidana Goodluck Jonathan.
“Na sha fada cewa muddin Jonathan yana nan, ba zan gabatar da kaina a kan takarar shugabancin kasar nan ba, sai dai idan ya yanke shawarar ba zai tsaya takara ba.
“Idan har za mu iya lallashinsa ya fito, zan tallafa masa da jinina. Saboda kunya, har yanzu bai shirya ba. Ina fatan za ku hadu da shi kuma ku karfafa shi ya tsaya.
“Zai yi aiki mafi kyau saboda yana da kwarewa. Mun san farashin abubuwa; mun san matakin hauhawar farashin kayayyaki.
“A lokacin mulkin Jonathan, ya kasance mai hada kai, yana magance matsalolin da suka shafi tsarin Almajiri da kuma samar da tsare-tsare ga matasa marasa aikin yi.
“Daukar nauyin jagoranci ya zama abin koyi. Muna bukatar shugabanni irinsa—matasa masu kuzari, hangen nesa, da tuki,” inji shi.
Mohammed ya ci gaba da bayyana cewa sukar da ya ke yi wa gwamnatin shugaba Bola Tinubu na daga cikin nauyin da ya rataya a wuyansa na taimakawa wajen dora kasar nan kan turba mai kyau.