Labaran Duniya

Hukumar Dake Kula Da Shirin Matasa Na Hidimtawa Kasa NYSC Ta Bankaɗo Wani Sirrin Kutse Da Akayi Hukumar

Shugaban hukumar kula da ma su yiwa kasa hidima ta NYSC, Janar Yusha’u Ahmed ya ce suna daukar matakan tsaftace hukumar sakamakon matsalolin da aka samu a baya, wadda ke kai ga sanya wadanda ba su yi karatu cikin masu yiwa kasa hidimar. 

Janar Ahmed ya bayyana cewar cikin irin wadannan sunaye da jami’oi ke gabatar musu harda wata mai sayar da biredi da Jami’ar Calabar ta gabatar da sunanta cikin wadanda za su yiwa kasar hidima. 

Shugaban ya ce wannan na daga cikin sunayen matasa 101 da jami’ar ta gabatar na wadanda ba su kammala karatun jami’a ba, domin sanya su cikin wadanda za su ci gajiyar shirin. 

Janar Ahmed ya jinjinawa shugabar jami’ar wadda ta yi tattaki da kanta zuwa ofishinsu domin gabatar da sunayen da aka saka ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button