Shan Miyar Ganyen Lalo Yayi Sanadiyar Mutuwar Akalla Mutane 12 A Jihar Zamfara
Kimanin mutum 12 ne suka rasa rayukan su a garin Ɗaki Takwas na karamar hukumar mulkin Anka da ke jihar Zamfara, bayan da ake zargin sun sha wata miyar Lalo mai ɗauke da guba.
Bayanai dai sunce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’ar da ta gabata, bayan da mutanen suka sarrafa miyar Lalo mai ɗauke da sinadarin maganin kashe ƙwari da wani manomi ya sanyawa gonar sa.
Tun da farko dai an gano cewar kimanin mutum 28 ne suka sha miyar, waɗanda suka fito daga gidaje biyu da ke garin, wanda ya zuwa yanzu wasu mutum 9 ke cigaba da karbar kulawar likitoci.
Daraktan da ke kula da yaɗuwar cututtuka a jihar Zamfara Dr. Yusuf Abubakar Haske, shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai, inda yace sauran mutanen tara suna ci gaba da karɓar magani a assibiti.
Hatsarin cin guba a cikin abinci dai ba baƙon al’amari ba ne a Najeriya, domin ko a ƴan kwanakin nan wata mata da ƴaƴan ta biyar sun rigamu gidan gaskiya a jihar Kano, bayan da suka ci wani ɗan wake da ake zargin yana ɗauke da guba a cikinsa.