Labaran Duniya

Rundunar Ƴan sandan Najeriya Tace Tana Zargin Shugaban NLC Da Tallafawa Wa Ta’addanci

Hukumar ƴansandan Najeriya ta gayyaci shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa, Joe Ajaero da ya bayyana gabanta domin amsa tambayoyi waɗanda ke alaƙa da zargin tallafa wa ta’addanci da take yi masa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin mataimakin kwamishinan ƴansanda ɓangaren jami’an tattara bayanan sirri.

Sanarwar da ta samu saka hannun Adamu Muazu, jami’in yaɗa labaru na hukumar, ta ce tana kuma zargin shugaban na NLC da kutse a intanet da kuma sauran abubuwa.

Hukumar ƴansandan ta yi barazanar cewa muddin bai amsa goron gayyata da ta yi masa ba, hakan zai janyo ta kama shi.

“Ofisihinmu na binciken Ajaero kan zargin haɗa baki don aikata zamba, tallafa wa ta’addanci, cin amanar ƙasa da kuma kutse a intanet,” in ji sanarwar da ƴansandan suka fitar.

Sanarwar ƴansandan ta ƙara da cewa ana son shugaban na NLC ya bayyana ne a gobe Talata 20 ga watan Agusta da misalin karfe 10 na safe domin amsa tambayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button