Labaran Duniya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Ya Amince Da Biyan Tallafin Man Fetur 

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bukatar kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) na yin amfani da ribar 2023 wajen biyan tallafin man fetur.

Shugaban kasar ya kuma amince da dakatar da biyan kudaden rikon kwarya na shekarar 2024 ga tarayya domin kara yawan kudaden da kamfanin man ke samu.

Duk da cewa Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a lokacin da yake jawabi a bikin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, alamu sun nuna cewa har yanzu gwamnati na kashe biliyoyin kudade wajen bayar da tallafin.

Sai dai a ko da yaushe Gwamnatin Tarayya tana musanta biyan tallafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button