Labaran Duniya

Shugaba Tinubu Yasha Alwashin Yin Amfani Da Ikonsa Domin Samarwa Sojoji Kayan Aiki Da Makamai

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin amfani da damar da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi wajen ci gaba da samar wa sojojin ƙasar, kayan aiki da makamai, domin gudanar da ayyukansu.

Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Juma’a lokacin bikin yaye hafsoshin soji da aka gudanar da kwalejin horas da manyan hafsoshin soji ta ƙasar da ke Abuja, kamar yadda mataimaki na musamman ga shugaban kan kafofin yaɗa labarai da sadarwar, Stanley Nkwocha ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar.

Bola Tinubu – wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima – ya amince da muhimmancin ingantaccen shugabanci wajen magance matsalar tsaro da sauran matsalolin da ke fuskantar Najeriya.

Shugaban ya koka kan halin da kwalejin horas da manyan hafsoshin ke ciki, inda ya alƙawarta samar wa kwalejin ci gaban da ya dace da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button