Labaran Duniya

Rundunar Ƴan Sanda Ta Kama Matar Da Ke Safara Harsashi A Galan Ɗin Manja

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Nasarawa ta yi nasarar cafke wata mata mai suna Hauwa Sani ɗauke da galan ɗin Manja shaƙe da harsashin jiragen yaƙi kimanin guda dari da ashirin da hudu da kuɗi N78,500 a hanyar Katsina.

Kakakin rundunar ƴan sanda jihar Ramhan Nansel, ya ce an kama matar ne tare da yarinya ƙarama yar shekara 2 a kauyen Doro na jihar Katsina kamar yanda Jaridar WIKKI TIMES ta ruwaito.

Nansel ya ce jami’an ‘yan sandan da ke aiki da sashen Keffi sun yi nasarar kama ta ne bisa sahihin bayanai da suka samu.

Ya ce wacce ake zargin ta karbo kayayyakin ne daga kauyen Rafin Sanyi da ke karamar hukumar Doma, jihar Nasarawa, zuwa jihar Katsina.

“A ranar 23/8/2024 bisa samun sahihan bayanai, jami’an ‘yan sanda yankin Keffi suka yi nasarar kama wata Hauwa Sani ɗauke da karamar yarinya a ƙauyen Doro, jihar Katsina.

“An sake ta ɗauke da alburusai dari da ashirin da hudu (124) maƙare a cikin galan din manja, wayar hannu daya, da kudi Naira78,500”.

“Bincike na farko ya nuna cewa wanda ake zargin ta karbo kayan ne a kauyen Rafin sanyi da ke karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa ta kuma koda su a cikin galan din manja ta,” cewar Nansel.

Ya ci gaba da cewa, yanzu haka dai an mika wacce ake zargin zuwa sashen tattara bayanan sirri na rundunar ƴan sanda da ke Abuja domin ci gaba da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button