Labaran Duniya

Yan Bindiga Na Cigaba Da Ta’azzarawa Al’umar Garin Sabon Birni Ta Jihar Sokoto

Rahotanni daga jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya, na cewa ‘yan bindiga a yankin Sabon Birni na ci gaba da satar jama’a masu dimbin yawa tare da kashe wasu.

Bayanan sun ce ‘yan fashin dajin na ci gaba da rike akalla mutum 150 baya ga karin wasu ashirin da takwas da aka sace a karshen makon nan a kauyen Makuwaana da ke karamar hukumar Sabon Birnin.

Wannan na zuwa ne kasa da mako guda da wasu masu garkuwa da mutane suka kashe Sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Muhammad Bawa.

Lamarin ya faru kwanaki bayan da wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da sarkin da dansa da wasu karin mutum shida a hanyarsu ta zuwa birnin Sokoto.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa Manema Labarai cewa suna cikin wani yanayi na zaman zulumi:

‘’Ba bu ranar da ‘yan bindiga ba su shigowa kauyuka, sansanonin da a garesu kewayen kauyukan suna daukar jama’a, ainihin ranar da aka yi sanarwar ba bu ran sarki, daddaren nan sai da suka shiga kauyen ‘yan Haru mai nisan kilomita biyu da sabon birni inda suka dauki mutum fiye 20 bayan mutum fiye da 10 da suka yi garkuwa da su”, in ji shi

Mutumin ya ce mazauna garuruwan Tsammaye da ungwar Lalle su na shirin tashi ya kuma yi ikirrain cewa ba bu wani ‘mataki da mahukuntan suka dauka’.

Sauran wuraren da maharan suka addaba a sabon birnin sun hada da kwanar maharba da Tursawa da sauransu

Sanata Ibrahim Lamido wanda dan majalisar dattawan Najeriya ne mai wakiltar Sokoto ta Gabas ya shaidawa Manema Labarai cewa akwai gaskiya a cikin alamarin:

”Wannan abu da ka ke ji gaskiya ce, har yanzu ‘yan taada suna nan a kauyukan Sabon Birni suna ta taadanci, suna daukar mutane, suna kai su daji suna garkuwa da su”

Sanatan ya ce ”karamar hukumar sabon birni ta zama kamar helkwatar ‘yan ta’ada ba wai in ce maka Sakoto kawai, a Najeriya kullun taadanci ake yi musu”

‘’Ina gaya maka garuruwan sabon Birnin da ke da wannan matsala sun kai tara a halin yanzu’’ in ji shi.

A wani labarin kuma ƙungiyar ci gaban gobirawa ta duniya ta yi kira ga gwamnati da ta taimaka masu wajen ganin an anso gawar sarkin na Gobir na Gatawa daga hannun ƴan bindiga.

Shugaban ƙungiyar Ibrahim Alhassan Sabon Birni ya ce su na son kamar yadda ake yi wa kowane musulmi sutura shima sarkin suna so ayi masa haka, inda ya kara da cewa rashin samun gawar ya sanya su cikin tashin hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button