Labaran Duniya

Kasar Nijar Zata Fara Tattara Bayanan Yanta’addaan ta’adda

Nijar
Bayanan hoto,…

Gwamnatin sojin Nijar ta buɗe rajista domin tattarawa tare da adana sunayen waɗanda ake zargi a ƙasar da harkokin ta’addanci, kamar yadda tashar talabijin na ƙasar RTN Tele Sahel ya ruwaito a jiya.

A wata doka da shugaban sojin ƙasar Birgediya Janar Abdourahmane Tiani ya sanya wa hannu, ta ce duk wani mutum da ya shiga rajistar, za a ƙwace kadarorinsa, a hana shi tafiya, sannan za a iya ƙwace shaidar zama ɗan ƙasar Nijar.

Za a sanya mutum ne idan yana taimakon ta’addanci ko dai shiga ciki ko tsarawa ko kasancewa cikin ƙungiyar ta’addanci ko aware ko wata ƙungiya da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar.

Laifukan da za a duba sun kunshi ɗaukar makami domin yaƙi da kasar, bayar da bayanan sirri ga ƙasashen waje, taimakon ƙasashen waje shigowa ƙasar da kuma fitar da wasu bayanai ko kalamai da za su iya tayar da zaune tsaye a ƙasar.

Tun bayan hamɓarar da Mohamed Bazoum daga mulki ne ƙasar take fuskantar ƙaruwar harkokin ta’addanci, inda aka fi kai hare-hare a kan sojin ƙasar, musamman a yankin Tillaberi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button