Labaran Duniya

Donald Trump Na Fuskantar Sabuwar Tuhuma Kan Yunƙurin Sauya Zaɓe

Tsohon shugaban Amurka Kuma dan Takarar kujerar Shugabancin Kasar a Karo Na biyu Donald Trump na sake fuskantar sabuwar tuhuma kan zargin sa da yunƙurin sauya sakamakon zaɓen 2020 bayan ya kayin da ya sha a wancan lokaci.

Wannan na zuwa ne bayan Kotun Kolin Amurka ta wanke Trump daga zargin, inda ta ce, yana da yalwatacciyar rigar kariyar da ke hana shi fuskantar tuhuma kan miyagun laifuka.

Tuni tawagar lauyoyi ƙarkashin lauyan gwamnati na musamman, Jack Smith ta ƙarɓi sabuwar tuhumar da ake yi wa Trump a birnin Washington, amma bisa dukkan alamu, zai yi wuya ta gurfanar da shi gabanin zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar nan da ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa, wato ranar da Trump ɗin na jam’iyyar Republican zai fafata da abokiyar hamayyarsa Kamala Harris ta Jam’iyyar Republican.

Wannan tuhumar da aka farfaɗo da ita na ƙunshe da tuhume-tuhume guda huɗu kamar dai yadda suka kasance a wancan tsohuwar tuhumar da masu shigar da kara suka yi wa Trump a bara.

Illa kawai sabuwar tuhumar na kallon Trump a matsayin ɗan takarar da ke neman kujerar shugabancin Amurka a karo na biyu, saɓanin a wancan tuhumar da aka ayyana shi a matsayin shugaban ƙasa.

A ranar 1 ga watan Yulin da ya gabata ne, Kotun Koli ta yanke hukunci kan tuhumar ta baya, inda ta bayyana Trump a matsayin wanda ke sanye da rigar kariya, abin da ke hana a hukunta shi kan wasu miyaagun laifuka da ya aikata a matsayinsa na wanda ke kan karagar mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button