Kungiyar Boko Haram Ta Ka Wani ƙazamin Hari A Wata Makarantar Yan Shi’a A Jihar Yobe
Wasu ‘yanta’adda da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne, da sanyin safiyar Juma’a, sun kashe dalibai a makarantar Faudiya mallakin ‘yan Shi’a da ke karamar hukumar Geidam a jihar Yobe.
Harin na ‘yan Boko Haram ya rutsa da makarantar Faudiya na kungiyar Harkar Musulunci ta (IMN), wacce aka fi sani da Shi’a a Najeriya.
Majiyoyi sun ce mayakan na Boko Haram sun mamaye unguwar Hausari da ke karamar hukumar Geidam da misalin karfe 3:44 na asubahin ranar Juma’a domin shirin su na kai harin a makarantar.
An ce ‘yan bindigar sun kai farmaki ne a lokacin da daliban ke barci.
Majiyar ta ce, “Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 3:44 na asuba, a lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki makarantar Faudiya wata fitacciyar makarantar ‘yan Shi’a da ke Geidam.
“Su (’yan bindiga) sun kai hari makarantar ne a lokacin da wadannan matasan ke barci suka kuma fito da su waje suka harbe su har lahira.
“Akwai tashin hankali da damuwa a garin bayan faruwar lamarin. Jama’a sun firgita da wannan mummunan lamari.” a cewar majiyar.
An kuma tattaro bayanai daga wasu ‘yan banga cewa an kashe ‘yan kungiyar Shi’a uku yayin da daya ya samu munanan raunuka.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ki bayar da cikakken bayani.