Rahotanni

DA ƊUMI-ƊUMI:🔥 Jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga 35 a wasu garuruwan jihar Zamfara

Daga: Yahaya Mahi Na Malam Babba

Sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar jama’ar gari da Askarawa sun aika ‘yan bindiga 35 lahira bayan wani kazamin artabu da suka gwabza a jihar Zamfara.

An tattaro cewa ‘yan bindigan karkashin jagorancin Jimmu Sumoli sun kaddamar da hari a garin Matuzgi da ke karamar hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara. A martanin da jami’an tsaro da mutanen garin suka yi ga maharan, sun gwabza a tsakaninsu wanda ya dauki tsawon sa’o’i biyu ana fafatawa.

A yayin arangamar, jami’an tsaro da mutanen garin sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 25, yayin da ‘yan bindigar suka kashe mutane uku a Matuzgi. Bayan kazamin fadan, sauran ‘yan bindigar sunyi yunkurin gudu, domin komawa maboyarsu.

Sahel24 Tv ta ruwaito cewa yayin da ’yan bindigar suka ja da baya, an yi musu kwanton bauna a kauyen Magamin Diddi da ke karamar hukumar Maradun. Wannan harin kwantan bauna ya yi sanadiyar mutuwar wasu ‘yan bindiga 10, wanda ya kai adadin ‘yan bindigar da aka kashe zuwa 35.

A ‘yan watannin da suka gabata, ‘yan bindigar sun kai wani hari makamancin wannan a garin na Matuzgi, inda suka yi garkuwa da wasu mutanen garin, suka kashe mutanen da suka sace, sannan suka sako mata daga cikinsu bayan an biya wasu makudan kudade.

A ranar 27 ga Agusta, 2024, an bayar da bayanan sirri game da shirin ‘yan bindigar na kai hari a garin na Matuzgi da Mai Jatau, inda aka ga babura kusan 40 sun nufi yankin. Matakin gaggawa na jami’an tsaro da mazauna kauyen ya yi matukar muhimmanci wajen dakile harin da kuma rage asarar rayuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button