Rahotanni

Kasar Amurka za ta sake aika ‘yan sama jannati bayan maƙalewar biyu a sama tun cikin watan Yuni

Amaurka za ta sake aika wata tawagar ‘yan sama jannati zuwa tashar ta sararin samaniya ta duniya.

To sai dai hukumar binciken sararin samaniyar ƙasar, NASA ta rage yawan ‘yan sama jannatin – da ke shirin wannan tafiya sararin samaniyar- domin bayar da dama ga wasu mutum biyu – da suka maƙale a tashar sararin samaniya tun cikin watan Yuni – su dawo.

A watan Satumba ake sa ran sake tura ‘yan sama jannatin – waɗanda ake sa ran saukowarsu cikin duniyarmu a cikin watan Fabrairu shekra mai zuwa tare da waɗanda suka maƙalen.

A cikin watan Yunin da ya gabata ne Suni Williams da Butch Wilmore Suka tafi ne da niyyar yin kwana takwas kawai, amma suka maƙale har yanzu .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button