Kasar Jamus ta kammala janye dakarunta daga Nijar
Kasar Jamus ta kammala janye ragowar dakarunta da suka rage a Jamhuriyar Nijar, a wani mataki na kawo ƙarshen ayyukan sojinta a yankin Sahel.
A jiya da maraicen ranar Juma’a ne dai wasu manyan jiragen dakon kaya biyar suka sauka a ƙasar Jamus ɗauke da sojoji 60 da ton 146 na kayan aikinsu daga Jamhuriyar ta Nijar.
Tun a cikin watan Mayu ne dai hukumomin na Nijar suka amince da ci gaba ayyukan sojojin Jamus a ƙasar har zuwa ƙarshen watan Agusta.
Yarjejeniyar ci gaba da aiki da juna ta citura tsakanini ɓangarorin biyu, bayan da Nijar ta kasa bayar da tabbacin kariya daga tuhuma ga dakarun na Jamus.
Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da jam’ian ƙasashen biyu suka fitar, sun ce ”janye dakarun ba shi ne ƙarshen haɗin gwiwa soji tsakanin ƙasashen ba”.
To sai dai sanarwa ta saɓa da kalaman da ministan harkokin wajen Jamus ya yi cikin watan Yuli cewa Jamus ba za sake haɗa kai da Nijar saboda abin da ya kira ”rashin amana”.
A shekarar 2016 ne Jamus ta fara aikin soji a Nijar, inda take da dakaru akalla 3,200 a ƙasar da ke yankin Sahel.