Labaran Duniya

RundunarƳansanda ta kama masu yiwa ƴan ta’adda safarar bindigogi a Jihar Katsina

Jami’an hukumar ƴansanda a jihar Katsina ta kama masu safarar bindigogi su 3 dake ɗauke da alburusan da ake kaiwa ƴa ta’adda a jihar.

Daily Trust ta rawaito cewa da ya ke jawabi ga manema labarai yayin holan waɗanda ake zargin, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce “a ranar 29 ga watan Agusta na 2024, da misalin karfe 1245, jami’an mu sun kama gawurtattun masu safarar mutane tare da kwato alburusai.

“An kama waɗanda ake zargin ne a karamar hukumar Dutsinma a yayin da suke yunkurin kai Alburusai 740 ga ƴan bindiga a dajin Yauni dake ƙaramar hukumar Safana.

“Binciken farko ya nuna cewa, waɗanda ake zargin sun karbi alburusan ne daga jihar Nasarawa domin kaiwa wani mai suna Harisu wanda gawurtaccen dan fashin daji ne.

” Mutanen uku sun amsa laifukansu, kuma sun bayyana sunan Harisu a matsayin wanda ya shirya safarar Alburusan”, inji shi.

Rundunar ƴan sandan ta ce tana aiki ba dare ba rana wajen kama masu aikata laifuka tare da gurfanar dasu gaban shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button