Rahotanni

Gwamna Dauda Lawal Ya Kai Ziyarar Jajantawa Ga Al’umar Garin Gummi Da Ambaliyar Ruwa Ta Rutsa Dasu

Daga: Shamsu Bello Bungudu.

A jiya Assabar be Gwamnan Jihar Zamfara ya kai ziyarar jaje ga waɗanda ibtila’in ambaliyar ruwa ya afka wa a Ƙaramar Hukumar mulkin Gummi. 

Yayin ziyarar Dauda Lawal ya zagaya inda gidaje suka rushe a cikin gari, sannan Kuma ya wuce garin Gayari dake gundumar Karamar Hukumar ta Gummi inda a chan ma ya ga irin asarar da aka yi. 

Tun bayan afkuwar lamarin, Gwamnatin Dauda Lawal ta tura da kwamishinoni nan take. Haka nan kuma mataimakin gwamna ma ya je washegari. 

“Sai dai a Cewar sa na aika da injiniyoyi waɗanda suka duba inda matsalar take, suka yi bincike sannan suka zo da bayanai na matakan da suka dace a ɗauka.” 

“Ya Kuma Kara da cewa A matsayin agajin gaggawa, na bada Naira Miliyan 100 na tallafi ga waɗanda ambaliyar ta rutsa. Sannan na aiko da buhu dubu goma na kayan abinci.”

Daga Karshe Gwamnan na jihar Zamfara, ya  bayar da umurnin a samar da filaye ga mutanen da ambaliyar ta shafa domin su gina gidaje a wuraren da babu barazanar ambaliya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button