Labaran Duniya

Bello Matawalle Da Wasu Manyan Sojoji Sun Isa Jihar Sokoto

Daga Shamsu Bello Lawal Bungudu.

Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle tare da Babban Hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa sun isa jihar Sokoto domin ba da gudummawa wajen murƙushe ƴan fashin daji da ke addabar yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya bai wa ministan da manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin mayar da ayyukansu zuwa Sokoto bayan ƙaruwar ayyukan ƴan fashin daji a baya-bayan nan da suka addabi Yankunan Sokoto Musamman gabashin Sokoto da Kuma jihar Zamfara dama yankin Arewa maso yamma Baki Daya.

Yazuwa yanzu dai shirye shirye na kankama domin Fara yakar Yan ta’addan da suke yawaita Kai faemake farmake da cin Karen su ba babbaka a kullun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button