Labaran Duniya

Kungiyar Kwadago Tace Shugaba Bola Tinubu Ya Saɓa Yarjejeniyar Da Suka Yi Da shi Kan ƙara farashin fetur

Kwamared Joe Ajero

Kungiyar ƙwadago a Nigeria (NLC) ta zargi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da karya yarjejeniyar da suka ƙulla kafin sanar da ƙarin farashin man fetur ranar Talata.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a yammacin yau Talata ta ce ɗaya daga cikin dalilan da suka sa suka amince da naira 70,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi a watan Yuli shi ne ba za a ƙara kuɗin fetur ba.

“Muna sane da zaɓin da shugaban ƙasa ya ba mu cewa ko dai a ba mu N250,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi [amma a ƙara farashin fetur zuwa N1,500 ko N2,000] ko kuma N70,000 [a bar farashin yadda yake],” a cewar NLC.

“Mun zaɓi na biyun saboda ba za mu juri a cigaba da azabtar da ‘yan Najeriya ba. Amma…yanzu ga shi ko sabon albashin ba a fara biya ba an sake zuwa mana da abin da ba za mu iya fahimta ba.”

Ƙungiyar ta bayyana ƙarin a matsayin “abin takaici” kuma “mai banhaushi”.

Da safiyar yau ne dai kamfanin mai na NNPCL na gwamnatin Najeriya ya sanar da sauya farashin daga N617 zuwa N897 kan kowace lita, abin da ya sa ‘yan Najeriya da dama suka nuna ɓacin ransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button