Muhammadu Buhari Ya Nemi A Dauki Mataki A Kan Waɗanda Suka Hallaka Mutane A Jihar Yobe
Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da mutanen da ‘yanbindiga suka kashe a jihar Yobe a farkon makon nan.
Wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawunsa, ya wallafa a shafukan sada zumunta ta ce harin na baya-bayan nan “mummunar tunatarwa ce ga mazauna yankuna cewa akwai babban aiki a gabansu da za su yi wajen taimakawa a daƙile matsalar ‘yanta’adda”.
Rahotonni daga jihar ta Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa an yi jana’izar mutum 30 da maharan masu iƙirarin jihadi suka kashe.
Cikin saƙon da ya aika wa Gwamna Mai Mala Buni da kuma majalisar sarakunan Yobe, tsohon shugaban ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan su, in ji sanarwar.
“Ya kuma nemi a ɗauki mummunan mataki kan waɗanda suka aikata wannan aikin rashin imanin.”
Sahel24 TV