Ruwan Sama Yayi Sanadiyar Rushewar Masallaci Mai Dimbin Tarihi A Kasar Nijar
Adadin yawan ruwan sama da ake ta samu ya rushe ɗaya daga cikin masallatai masu ɗimbin tarihi a Jamhuriyar Nijar, kamar yada mazauna yankin suka faɗa.
Shahararren ginin masallacin na laka a Zinder, wanda aka gina a tsakiyar ƙarni na 19, “ya shafe gaba daya daga taswira a jiya bayan da aka yi ruwan sama mai yawa”, in ji Ali Mamane a ranar Laraba.
Tun a watan Yuni ne ake fama da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Jamhuriyar Nijar wanda ya haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da jikkata wasu dubbai.
Masallacin wanda ya zama alamar yin fice ga birni na biyu a Jamhuriyar Nijar, wanda ya taba zama babban birnin kasar mai karfin fada a ji, ya ruguje a ranar Talatar da ta gabata, inda aka rika watsa bidiyon mummunan lamarin a kafafen sada zumunta na intanet.
Masallacin wanda aka yi shi da laka da azara, ya kasance na biyu da aka fi yawan ziyarta a Nijar bayan masallacin Agadez wanda ke cikin jerin UNESCO, a cewar ma’aikatar yawon bude ido ta Nijar.
El Hadj Mansour Kakale, wani shugaban addini na yankin ya ce “Daruruwan shekaru masu ibada suna zuwa daga nesa da ko ina don yin addu’a a duk ranar Juma’a da kuma tarukan Musulunci.”
“An gaya mana cewa ya wasu ɓangarorinsa sun tsattsage, amma ba mu iya yin komai ba saboda ruwan sama,” wani jami’in ya shaida wa gidan talabijin na kasar.
Fadin yankin kudu maso gabashin Zinder na daga cikin wadanda aka fi fama da mamakon ruwan sama a kasar.
A cikin kasa da watanni uku, ambaliya ta yi sanadin mutuwar mutum 217, sannan wasu 200 suka jikkata, yayin da lamarin ya shafi wasu 300,000 a fadin kasar ta Nijar, a cewar alkaluman da gwamnati ta fitar daga ranar 22 ga watan Agusta.
A bisa ka’ida daga watan Yuni zuwa Satumba, daminar Nijar takan haifar da asarar rayuka, inda mutum 195 suka mutu a shekarar 2022.
Masana kimiyya sun dade suna yin gargadin cewa sauyin yanayi da gurɓataccen hayakin mai ke haifar da matsanancin yanayi kamar ambaliyar ruwa da yawa, mai tsanani da kuma daɗewa.