Alhaji Haruna me riga ya bada tallafin makudan kudi ga Al’umar Unguwar Galambi
Sakataren zartarwa na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa Dr Haruna Mai riga ya bada tallafin kudi na kashin kansa na naira miliyan daya da dubu dari biyu, ga masu karamin karfi a unguwar Galambi domin gyara muhallinsu da kuma yin sana’oi.
Ya ce wadanda suka amfani rukuni hudu ne ko wanne rukuni akwai adadin mutane 40 da zasu amfana da naira dubu dari uku.
Dr Haruna Mai riga ya ce ya basu tallafin ne dan ya taimaka musu su zama masu dogaro da kansu, kasancewar ana cikin wani yanayi
A jawabinsa shugaban jam’iyar APC na KH Gwaram Ayuba Umar Nasarawa ya yabawa sakataren bisa tunanin sa na ganin an tallafa musu a daidai lokacin daya dace, Inda ya bukaci wadanda suka amfana da suyi amfani da kudaden ta hanyar data dace.
Wasu da suka amfana da tallafin Malam Muhammadu da Malama Harira sun godewa Dr, Haruna Mai riga bisa tallafin daya basu tare da yin alkawarin amfani da kudaden ta hanyar data dace.