Labaran Duniya

Kamfanin NNPCL ya ce kowa na da damar sayen mai a matatar Dangote

Babban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya musanta zargin da ya ce ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Najeriya, MURIC ta yi masa na yi wa matatar mai ta Dangote maƙarƙashiya.

MURIC ta yi zargin cewa ƙarin kuɗin mai da NNPCL ya sanar a baya-bayan nan zai hana matatar Dangoten sayar da man a farashi mai rahusa, sannan ta yi zargin cewa kamfanin NNPCL ne kawai zai riƙa sayen mai daga matatar.

To sai dai cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Asabar, ya musanta zargin, yana mai cewa kasuwa ce ke ƙayyade farashin man kowace matata ciki kuwa har da ta Dangote.

”Ƙarin kuɗin mai da aka samu a baya-bayan nan ba zai hana matatar Dangote ko duk wata matata a cikin ƙasar nan samun ciniki ba. Idan ma suna ganin kamar kuɗin ya yi yawa, to matatar ta samu damar da za ta rage farashi domin samun ciniki a kasuwa”, in ji sanarwar.

Haka kuma NNPCL ɗin ya ce babu tabbacin samun ragin farashi kan man da aka tace a gida fiye da yadda ake sayar da shi a kasuwar duniya, kamar yadda matatar Dangoten ta tabbatar masa.

Kamfanin NNPCL, ya ƙara da cewa zai sayi man Dangote ne kawai idan farashin man a kasuwar duniya ya fi yadda ake sayar da shi a Najeriya, don haka matatar Dangote da sauran matatun cikin gida na da damar sayar da man ga duk wanda ke buƙata a kan farashin da suka daidaita.

”NNPCL ba shi da niyyar kankane sayar da man shi kaɗai a fagen kasuwancin da kowa ke da damar shiga a dama da shi, don haka maganar a ce NNPCL ne zai sayi mai daga matatar ba ta taso ba,” in ji sanarwa.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button