Ƙungiyar IZALA ta tara Naira miliyan ɗari da sha biyu ( ₦ 112,000,000.00) a wajen tattara fatun layyan da ta gabata na shekarar 2024/1445H
Daga: Ibrahim Baba Suleiman
Ƙungiyar IZALA ta tara kudi na fatun layya da resitai da jimallar su yakai adadin Naira miliyan ɗari da sha biyu ( ₦ 112,000,000.00), wajen tattara fatun layyan bana da resitai da jama’a suka taimaka a layyar shekarar 2024/1445H
Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau, shine ya sanar da hakan bayan ya karbi rahoton kwamitin wanda shugaban kwamitin Malam Lamara Azare ya bada a asabar ɗinnan a garin Dutse ta jahar Jigawa.
Sheikh Bala Lau ya yabawa jama’a da sukayi hobbasa wajen ganin sun mika fatun layyan su ga kungiyar IZALA, ya kuma sha alwashin ci gaba da ayyukan raya addini kamar yadda aka Saba da kudaden a baya, ta yadda koda wanda ya bada ya koma ga Allah, zaici gaba da samun lada Mai gudana daga Allah SWT.
An gabatar da rahoton ayyukan kwamitin a gaban Shugabanni da jiga-jigan Malaman Ƙungiyar a taron majalisar ƙasa da ƙungiyar ta gabatar a birnin Dutse a jahar Jigawa.
1-A Bana jahar Sokoto ita tazo ta farko, inda ta samar da: Naira Miliyan goma sha huɗu da dubu ɗari shida da arba’in da biyar da ɗari bakwai da naira biyar kacal.
₦ 14,645,705.00
2-Jahar Kaduna ita tazo na biyu inda ta tara:
₦12,109,800.00
3-Jahar Kebi ita tazo na uku ta tara:
₦11,506,900.00
4-Jahar Bauchi ita tazo na hudu ta tara:
₦ 7,829,582.50
5-Jahar Katsina ita tayi na biyar ta tara:
₦ 7,234,625.00
6-Jahar Zamfara ita tayi na shida ta tara
₦6,707,200.00
7-Jahar Taraba ita tayi na bakwai ta tara:
₦6,554,825.00
8-Jahar Niger ita tayi na takwas ta tara:
₦ 5,537,800
9-Jahar Adamawa ita tayi na tara ta tara:
₦5,290,500.00
10-Jahar FCT Abuja ita tayi na goma ta tara:
₦4,572,250.00
11-Jahar Jigawa ita tayi na goma sha ɗaya ta tara:
₦3,535,287.50
12-Jahar Nasarawa ita tayi na goma sha biyu ta tara:
₦ biyu 3,530,850.00
13-Jahar Kano ita tayi na goma sha uku ta tara:
₦3,330,290.00
14-Jahar Gombe ita tayi na goma sha huɗu ta tara:
₦ 3,004,100.00
15-Jahar Kogi ita tayi na goma sha biyar ta tara:
₦2,952,350.00
16-Jahar Lagos ita tayi na goma sha shida ta tara:
₦2,901,334.00
17-Jahar Plateau ita tayi na goma sha bakwai ta tara:
₦2,467,350.00
18-Jahar Borno ita tayi na goma sha takwas ta tara:
₦2,222,600.00
19-Jahar Benue ita tayi na goma sha tara ta tara:
₦1,295,600.00
20-Jahar kwara ita tayi na ashirin, ta tara:
₦1,097,919.00
21-Jahar Yobe ita tayi na ashirin da ɗaya ta tara:
₦875,185.00
22-Jahar Oyo ita tayi na ashirin da biyu inda tara:
₦840,248.30
23-Jahar Ogun ita tayi na ashirin da uku ta tara:
₦430,080.00
24-Jahar Rivers ita tayi na ashirin da huɗu ta tara:
₦ 324,450.00
25-Jahar Osun ita tayi na ashirin da biyar ta tara:
₦287,878.70
26-Jahar Delta ita tayi na ashirin da shida ta tara:
₦165,000.00
27-Jahar Omdo ita tayi na ashirin da bakwai ta tara:
₦145,790.00
28-Jahar Edo ita tayi na ashirin da takwas ta tara:
₦140,000.00
29-Jahar Anambra ita tayi na ashirin da tara ta tara:
₦101,000.00
30-Jahar Ebonyi ita tayi na talatin ta tara:
₦83,500.00
31-Jahar Akwa Ibom ita tayi na talatin da ɗaya ta tara.
₦64,100.00
32-Jahar Cross Rivers ita tayi na talatin da biyu ta tara:
₦ 53,500.00
33-Jahar Enugu ita tayi na talatin da uku ta tara:
₦53,000.00
34-Jahar Abia ita tayi na talatin da huɗu ta tara:
₦40,000.00
35-Jahar Imo ita tayi na talatin da biyar ta tara:
₦25,000.00
36-Jahar Ekiti ita tayi na talatin da shida ta tara:
₦25,000.00
37-Jahar Bayelsa ita tayi na ƙarshe inda tayi na talatin da bakwai, ta tara:
₦20,000.00
~JIBWIS NIGERIA