Rahotanni

Bello Turji ya rage farashin kuɗin haraji da ya azawa al’ummar Garin Moriki

Shahararren ɗan ta’adda Bello Turji ya amince al’ummar Moriki na jihar Zamfara su biya naira miliyan 30 maimakon miliyan 50 da ya bukuta, a matsayin kudin diyya.

Bello Turji dai ya tilasta al’ummar garin su biya waɗannan maƙudan kuɗin zuwa ranar Laraba, biyo bayan kashe masa shanu da sabon kwamandan sojojin yankin yayi.

Barista Audu Bulama Bukarti ya wallafa a shafin sa cewa, an buƙaci ko wane magidanci da ya bayar da naira dubu 10, yayin da waɗanda ba su da aure za su biya naira dubu 2 duk kuwa da yunƙurin hana ba da waɗannan kuɗaɗen da kwamandan sojojin yayi.

Sahel24 Tv

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button