Rahotanni

Daya Daga Cikin Jiga jiganln jam’iyyar APC ya roƙi Tinubu da ya yi gaggawar ceto talakawan Najeriya

Daga: Lukman Aliyu Iyatawa

Wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Osun Olatunbosun Oyintiloye ya roƙi shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yi gaggawar ceto talakawan Najeriya daga mawuyacin halin da suke ciki.

Oyintiloye ya ce halin da ƴan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu ya sanya ya zama wajibi shugaban ƙasar ya gaggauta yin aiki da dabarun da za su kawo sauƙin rayuwa ga al’umma cikin gaggawa.

Oyintiloye wanda tsohon ɗan Majalisa ne ya bayyana ƙwarin gwiwa kan ƙoƙarin Shugaba Tinubu cewa zai iya rage raɗaɗin da talakawa ke ciki a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi a Osogbo.

Sai dai ya ba da shawarar a yi amfani da dabarun da za su kawo ɗauki cikin gaggawa saboda halin matsin da ake ciki.

Ya kuma yi nuni da irin matsin tattalin arzikin da talakawa ke fuskanta a halin yanzu a sabili da ƙarin farashin Man Fetur, wanda kuma hakan ya haifar da hauhawar farashin kayan masarufi, da farashin iskar gas na dafa abinci da sauran muhimman abubuwan amfanin yau da kullum ga ƴan Najeriya.

Ya ce ƙarin farashin Man Fetur da aka yi a baya-bayan nan ya ƙara tsananta wahalhalun da talakawan Najeriya ke fama da su.

A cikin kalamansa yace “ƴan Najeriya na fatan ganin an samu sauyi mai kyau a ƙasar nan, amma dole ne gwamnati ta hanzarta ɗaukar matakan cimma wannan buri”.

Dimokuradiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button