Rahotanni

Haɗarin wata Babbar mota ya hallaka mutane 13 da jikkata 45 a Kasar Cote d’Ivoire

Aƙalla mutane 13 ne suka ƙone ƙurmus a arewacin Cote d’Ivoire bayan da wata motar fasinja da ta taso daga Mali ta yi taho mu gama da wata motar dakon man fetir, inda wasu 45 suka jikkata.

Hatsarin ya faru ne a cikin daren Juma’a a kan babbar hanyar da ta haɗa Bouaké da Korhogo, manyan biranen biyu da ke arewacin ƙasar Cote d’Ivoire.

Ƴan sanda sun ce mutane 45 sun jikkata ciki har da yara 19 waɗanda suke samun kulawa a asibitocin yankin.

RFI Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button