Matashin da ya yi wa yarinya ƙarama fyaɗe a Jihar jigawa ya shiga hannu
Daga: Ashiru Usman Sabuwar Gwaram
Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta yi nasarar cafke wani matashi mai suna Bashir Umar mai shekara 32 ɗan asalin Unguwar Galamawa dake ƙaramar hukumar Dutse, wanda ya yi amfani da Almakashi da cokali ya sanya a cikin farjin wata ƙaramar yarinya.
Haka kuma ya sanya mata sirinji a gaban ta wanda hakan yasa jini ya ɓalle mata har ta galabaita.
Bayan ta dawo hayyacin ta sai shi wanda ake zargi wato Bashir ya bata kuɗi Naira ɗari da hamsin, kuma ya zare mata ido yace idan ta faɗa a gida zai kashe ta ya kashe iyayen ta, hakan yasa taji tsoro taki faɗa a gida kullum yana tsayawa a hanya idan zata je makaranta yayi mata abinda ya saba.
Bayan iyayen ta sun fahimci ta samu matsala fitsari da ba haya yana haɗuwa ya fito mata a lokaci guda sai suka kaita asibi, da zuwa asibiti ne likitoci suka tabbatar da cewa an lalata mata farji.
Yanzu haka dai matashin yana tsare a hannun ƴan sandan kafin a kammala bincike dan turashi zuwa kotun ya girbi abunda ya shuka.