Labaran Duniya

Matsaran iyakokin Najeriya sun koka dangane da rashin biyansu hakkokinsu

Jami'an tsaron Najeriya masu kula da kan iyaka

Wasu jami’an tsaro da ke aikin kula da kan iyakokin Najeriya, sun fada cikin mawuyacin halin rayuwa, sakamakon rashin biyan su kudaden alawus na tsawon shekara biyu da rabi.

Jami’an tsaron da suka hada da hukumomin kwastam da na masu kula da shigi da fice na Najeriyar, sun ce sun kwashe shekara biyar suna gudanar da wannan aiki, tun zamanin gwamnatin da ta gabata.

Daya daga cikin jami’an tsaron da abin ya shafa ya yi, ya shaida wa BBC cewa gaskiya suna cikin matsala sosai saboda an kai su wuraren da suke aiki wato kan iyakokin Najeriyar ne tun lokacin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce, ” A lokacin da aka kai mu wajen an kai mu ne tare da sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an tsaro na DSS, baya ga jami’an kwastam da na Immigration wato masu kula da shige da fice, ana biyansu kudaden alawus akan kari, to amma daga baya abin ya gagara”.

“Tun a lokacin gwamnatin shugaba Buhari sai da muka yi wata 18 ba a biya mu alawus ba, abin damuwar ma shi ne yawanci idan an kai mutum irin wadannan wurare ba a wuce shekara biyu zuwa biyu da rabi, amma mu a yanzu mun kasance a kan iyakar nan har tsawon shekara biyar.”

Jami’in tsaron ya ce, “A yanzu watanmu 30 ba kudi, ga kuma matsalar tsaro da kasarnan kef ama da ita, a hanyar Kwara har abokan aikinmu ‘yan fashin daji sun sace da kuma kisan wasu.”

Ya ce, “Saboda irin wannan yanayi da muka shiga na rashin biyanmu alawus tsawon watanni ya sa wasu gurbatattu daga cikinmu ma sun shiga hannu dumu-dumu cikin batun rashin tsaro.”

“Mu bama fatan haka ta faru damu, kuma muna tsayawa mu y iwa kasarmu aiki cikin amana saboda muna da baya.”

Jami’in tsaron, ya ce saboda rashin biyansu alawus kafin ayi albashi ma sun ci bashin da ya yi musu katutu, saboda albashin bashi da yawa ba isarsu yake ba.

Ya ce, “Ya kamata a dubi halin da muke ciki wata 30 muna bin bashin alawus, alhali ana biyan wasu jami’an tsaron da ke wurare irinsu Maiduguri.Sojojin da ke aiki a can ana biyansu hakkokinsu, mu me muka yi? gashi an kai mu cikin kurgurmin daji inda ‘yan bindiga suke.”

“Yanzu gamu cikin fargaba, ga babu alawus ga kuma wahala, sannan sai mu kwashi lokaci ko gida muje ga iyalanmu bama yi, sai iyalinka ya yi ciwo ya warke sai dai a waya.”

Jami’in tsaron y ace, “Mu yanzu abin da muke so shi ne muna kira ga hukumar Kwastam da ta Immigration da ma duk wani mai hannu a wannan aiki da aka kai mu, a dubi Allah a dubi matsalar da muke ciki, ga yanayin tsadar rayuwa a biyamu hakkokinmu.”

Sannan kuma ya kamata a canja mana waje domin aiki irin wannan da ake kai mutum ba a daukar dogon lokaci, amma mu namu shekara biyar ai ya zama wahala, in ji shi.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button