Al'ajabi

Akalla Sama da mutum 26 ne suka mutu bayan kifewar jirgin ruwa a Senegal

...

Mutane 26 ne suka mutu bayan da wani jirgin ruwa dauke da bakin haure ya kife a gaɓar tekun Senegal.

Hukumomi sun ce sama da mutane ɗari ne ke cikin jirgin ruwan kamun kifin a lokacin da ya nutse bayan ya yi tafiyar kilomita huɗu kacal.

An ceto mutane huɗu kuma ana ci gaba da gudanar da aikin ceto domin lalubo waɗanda suka yi ɓatan dabo.

Jirgin ruwan ya taso ne daga Mbour mai tazarar kilomita 80 kudu da Dakar babban birnin ƙasar, inda ya nufi tsibirin Canary na ƙasar Sifaniya da ke gaɓar tekun yammacin Afirka.

Ƙasar Senegal na ganin ƙaruwar jiragen ruwa ɗauke da ƴan ci-rani da ke ƙoƙarin ƙetarawa zuwa tsibirin Canary na ƙasar Sifaniya, inda aka samu baƙin haure kusan dubu talatin da suka yi wannan balaguron a bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button