Labaran Duniya

Atiku Abubakar ya soki Tinubu kan ƙoƙarin tauye haƙƙin ƙungiyoyin jama’a da kafafen yaɗa labarai

...

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana matukar damuwarsa game da abin da ya kira a matsayin cin zarafin ƙungiyoyin fararen hula da masu fafutuka da kafafen yaɗa labarai a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

A wata sanarwa da Atiku ya fitar a shafinsa na X, ya kwatanta irin yanayin da ake fama da shi a halin yanzu da mafi tsananin kwanaki na mulkin kama-karya na sojoji, yana mai nuna fargaba kan yadda gwamnati ke ƙara tauye haƙƙin jama’a da ƙara dabarunta na tsoratarwa.

Atiku ya ce “Kamen da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero misali ne ƙarara na kokarin da gwamnatin ke yi na rufe bakin ƙungiyoyin fararen hula da na ƙwadago.”

“Wannan matakin wani ɓangare ne na fafutukar da gwamnatin ke yi na tsoratar da manyan muryoyin jama’a a Najeriya.” in ji Atiku.

Atiku ya soki batun ƙaruwar barazanar ‘yancin ‘yan jarida.

Ya kuma bayyana matakin DSS na mamaye ofishin SERAP a matsayin cin zarafi ga kimar dimokraɗiyya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta karkata akalarta daga murkushe ƙungiyoyin farar hula zuwa magance matsalar tsaro da ke addabar ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button