An Tabbatar Da Rasuwar Wani Matashi Bayan Da Aka Zargi Ya Rataye Kan Sa Ne A Jihar Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce waní matashi rnai suna Umaro Garba ɗan unguwar Jar-Kuka mai shekaru 32 a Duniya, an yi zargin ya rataye kan sa da wani tsumma a sama al’amarin da ya yi sanadiyyar rasuwar sa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar wa Dala FM faruwar al’amarin a ranar Talata 10 ga watan Satumban 2024.a
Ya ce sun samu rahoto ne daga wani mutum daga unguwar Jar-Kuka, da ya ce sun ga ƙanen sa rataye a sama da Tsumma a ranar 8 ga watan Satumban 2024, lamarin da Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba, ya bai baturen ƴan sandan na Mariri umarni domin kai ɗaukin gaggawa, inda suka garzaya unguwar da al’amarin ya faru tare da sakko da shi daga saman da ake zargin ya rataye kan nasa.
A cewar sa, “Bayan da jami’an namu suka sakko da matashin suka kai shi babban Asibitin Sir. Muharnnadu Sunusi lamarin da Likata ya tabbatar da rasuwar sa, “in ji Kiyawa”.
Abdullahi Haruna ya ƙara da cewa tuni suka miƙa gawar marigayin ga ƴan uwansa kuma suka yi jana’izar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Manema Labarai dai sun ruwaito cewa, SP Kiyawa ya kuma ce yanzu haka sun dukufa wajen faɗaɗa bincike akan dalilan da suka sanya matashin ya rataye kan nasa har ya rasu.
Kiyawa ya kuma shawarci al’umma, da idan suka lura da wani baƙon al’amari akan ɗan uwan su musamman ma na keɓancewa a wuri guda, ko alamun suna cikin damuwa, da su rinƙa jan su a jiki domin gujewa ta’addar kashe kai daga wasu suke yi, saboda wani dalili nasu.