Labaran Duniya

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce ƴansanda 32 Da Bindigogi 5 ke tsaron ƙauyuka 200 a jihar Katsina.

A hirarsa da DW Hausa, gwamnan ya ce bindigogi tara ake baiwa ƴansandan, kuma a halin yanzu biyar daga cikin bindigogin ne suke aiki.

Ya ce: “A yanzu haka a Jihar Katsina akwai karamar hukuma mai ’yan sanda 39 da bindigogi guda tara, waɗanda biyar daga bindigogin ne suke aiki,” in ji Dikko Radda.

Duk da cewa bai ambaci suna ba, amma ya ce, “Karmar Hukumar tana da gundumomin siyasa 10, tare da kauyuka sama da 200.

Makon da ya wuce ne gwamna Dikko Radda ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su ɗauki matakan kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ke nuna yadda tura ta kai bango kan girman matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button