Wasanni
Rikici Ya Barke A Tsakanin Mbappe da PSG Kan Albashi
Ɗan wasan ƙwallon ƙafa Kylian Mbappe ya yi watsi da tayin da hukumar ƙwallon ƙafar Faransa ta yi masa na shiga tsakani a rikicin albashi da ya kaure tsakaninsa da tsohuwar ƙungiyarsa ta Paris Saint-Germain.
Ɗan wasan na Real Madrid ya ce yana bin PSG bashin kusan dala miliyan 60 a matsayin albashi da alawus-alawus, wanda ƙungiyar ta ce ɗan wasan ya amince cewa zai yafe idan har zai bar ta a kyauta.
Ɗan wasan mai shekara 25 ya koma Madrid ne a wannan bazarar a matsayin ɗan wasa mai zaman kansa bayan ƙarewar kwantiraginsa da zakarun na Faransa.
Lauyoyin ɓangarorin biyu sun gana da kwamitin shari’a na gasar Ligue 1 ta Faransa a ranar Laraba ba tare da cim ma matsaya ba.
Yanzu tana unanin lamarin zai ƙare ne a kotu.