Ƙungiyoyin Arewacin Najeriya sun zaɓi sabon shugaban su daga Zamfara
Daga: Yahaya Mahi Na Malam Babba
Manyan ƙungiyoyin Arewacin Najeriya masu zaman kansu, sun tabbatar da shugabancin Matashin ɗan kasuwa Nabil Shinkafi, a matsayin Shugaban Matasan Arewa, inda suka bashi takardar shedar shugabanci (Certificate) kuma sun karrama shi da lambar yabo.
Manyan kungiyoyin Matasan Arewa Youth Leadership groups sun karrama matashin ɗan kasuwar Nabil Shinkafi a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagorori masu son ci gaban mutanen Arewacin Najeriya, ta hanyar samar masu da abin yi, da kuma inganta iliminsu.
An yi taron karrama matashin a jiya Talata, a babban birnin tarayya Abuja.
Matashin ɗan asalin karamar hukumar mulkin Shinkafi ta jihar Zamfara dai, ya himmantu wurin bayar da tallafi ga gajiyayyu da marasa galihu na arewacin Najeriya da duniya baki daya.
Da yake jawabi bayan kammala bikin Matashin yayi godiya ga Allah a kan wannan muƙami sannan ya yi kira ga sauran al’umma da su tayashi addu’a a kan Allah ya kara masa kwarin guiwa akan wannan jagoranci.