Har yanzu ba a ga mutum 40 da kwale-kwalensu ya kife ba a Zamfara
Hukumomi a jihar Zamfara na cewa har yanzu ana ci gaba da aikin ceto mutum fiye da 40 da kwale-kwalensu ya kife a garin Gummi na jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne ranar Asabar da safe lokacin da kwale-kwalen ya kife da kusan mutum 50 a cikinsa galibinsu mata da ƙananan yara da ke kan hanyarsu ta zuwa gonaki.
Daraktan hukumar kare aukuwar bala’o’i ta jihar Dakta Hassan Usaman Duran ya tabbatar wa BBC cewa zuwa yanzu ba a ga mutum fiye da 40 ba, bayan kifewar kwale-kwalen.
“A lokacin da lamarin ya faru an ceto mutum bakwai, kuma daga baya an lalubo gawar mutum biyu, daga nan kuma har yanzu ba a iya gano kowa ba tukunna,”in ji shi.
Shi ma shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Amb. Bala Ahmad ya shaida wa Manema Labarai cewa jami’ansu na ci gaba da aikin ceto domin zaƙulo ragowar mutane fiye da 40 da har yanzu ba a gani ba.
Lamarin dai ya tayar da hankulan mutanen yankin, yayin da wasu ‘yan’uwa suka fitar da rai daga ceto ‘yan’uwan nasu a raye.
Sahel24 Tv